Arewa News Update
17/02/2026
Da ɗumi-ɗumi: Sowore ya tabbatar da zargin El-Rufa’i kan shigo da sinadarin guba Najeriya Yace an fara amfani da gubar a kansu.
Dan gwagwarmaya a fannin siyasa, Omoyele Sowore, ya ce zargin da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi na cewa an shigo da sinadarin guba mai suna thallium sulphate zuwa Najeriya ya fara tabbata bisa alama.
Sowore ya bayyana hakan ne yayin wata zanga-zanga da suke gudanarwa a harabar Majalisar Ƙasa kan batun dokar zaɓe, inda ya yi ikirarin cewa jami’an ‘yan sanda sun harba musu wani irin gas da ba barkonon tsohuwa ba ne k**ar yadda aka saba amfani da shi wajen tarwatsa masu zanga-zanga.
Ya ce abin da aka harba musu na iya kasancewa wani nau’in guba, yana mai ƙara da cewa tun da farko El-Rufa’i ya yi gargadin cewa an shigo da sinadari mai matuƙar haɗari cikin ƙasar.
Haka kuma ya tunatar da cewa tsohon gwamnan ya rubuta wasiƙa ga mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, domin neman ƙarin bayani kan dalilin shigo da wannan sinadari.
Har zuwa yanzu dai hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye da ke tabbatar ko musanta zargin ba, lamarin da ke ƙara jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ‘yan ƙasa.
15/02/2026
Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, zai jagoranci babbar tawagar gwamnatin tarayya zuwa Kano bisa umarnin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin jajantawa da kuma tallafa wa waɗanda gobarar kasuwar Singa ta shafa.
Mai bai wa shugaban kasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, da ya sanar da haka a ranar Lahadi, ya ce tawagar, wadda za ta taso daga Abuja gobe, za ta miƙa saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa ga yan kasuwar da s**a yi asarar biliyoyin Naira sak**akon gobarar da ta tashi a kasuwar.
A madadin gwamnatin tarayya, tawagar za ta kuma yi alƙawarin bayar da tallafin kuɗi domin taimaka wa ƴan kasuwar da abin ya shafa, tare da tallafa wa gwamnatin jihar Kano wajen gaggauta buɗe kasuwar domin komawa harkokin kasuwanci.