Da'irar Azare

Da'irar Azare

Share

06/06/2022

“A Sakonnin Imam Khomeini (QS) ya yi ta amfani da Kalmar ‘Mustad’afin’ (raunanan da ake zalunta), raunanan mutane na ko ina, ba a ce maka wadanda ake zalunta din Musulmi kawai ba, Musulmi ne ko Kirista, zalunci bashi da kyau a kan kowa. Ba a goyon bayan zalunci a kan kowa.

“Wato mu bamu yarda da zalunci ba ko a kan wane ne, hatta ko da azzalumi aka zalunta, za mu ce wannan kam an zalunce shi, domin muna so a yi masa adalci. Misali, da za a k**a shi, sai a ce a yi masa wani hukunci wanda ya wuce laifin da ya yi, za mu ce an masa zalunci. Allah Ta'ala yana cewa: “Ku yaki masu yakarku a tafarkin Allah, amma kar ku yi shisshigi, Allah baya son masu shisshigi.” (Baqara: 190).

“Ko mutum yana yakarka ne, ko abokin gabanka ne, ba a ce ka masa shisshigi ba, ba a ce ka zalunce shi ba. Wannan nizamin addini kenan. To sai ya zama Imam ya ta jaddada cewa “A tallafawa wadanda ake zalunta ko su wane ne.”

— Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabinsa na Tunawa da Imam Khomeini (QS) karo na 33 a shekarar 2022.

Photos from Da'irar Azare's post 02/05/2022

An Nuna Goyon Bayan Palastine A Da'irar Azare A Masallacin Idi.

Ayau Litinin 1 ga watan Shawwal dai-dai da 02-May-2022 Yan uwa Musulmi Almajiran Sheikh Zakzaky (H) sun gudanar da Muzahara zuwa Masallacin Idi, Muzaharar da aka fara gudanarwa ta fara daga kofar gidan Wakilin Yan uwa na Garin Malam Aliyu Abubukar Dawod k**ar yadda aka saba duk shekara.

Tawagar Yan Uwan sun rike banners masu dauke da Foton Jagora Sheikh Zakzaky tare da Tutocin kasar Palastine domin nuna goyon baya ga raunanan Palastine din, Gefe guda masu jerin gwanon sun yi kira ga Gwamnatin Nigeria akan ta gaggauta sakarwa Malamin Passport din sa domin ya samu damar Fita neman magani.




*MediaForumAzare

Want your business to be the top-listed Beauty Salon in Azare?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Category

Telephone

Website

Address

Matsango
Azare
07046431819