BRC Azare 94.6 Fm station
03/06/2024
Albishirin Ku masu Sauraron wannan tasha mai Albarka, Idan Allah ya kaimu ranar Asabat mai zuwa 8 ga watà n June, zamu fara kawo muku shiri na musamman kan kiwon lafiya Mai suna "Lafiya Ginshikin Rayuwa" Shirin Hadin guiwa tsakanin Hukumar BRC fm Azare da kuma kungiyar likitoci ta Residents Doctors reshen FMC Azare s**a dauki nauyi.
Ku cigaba da Sauraron tashar BRC fm Azare a kowanne lokaci.
04/03/2024
Azumin Ramadhan : Sarkin Kano Aminu Ado Bayero Ya Roki 'Yan Kasuwa Su Rage Farashin Kayan Abinci
A wajen kaddamar da littafin tarihin "Daulolin Kasar Hausa" wanda Farfesa Sa'idu Muhammed Gusau ya wallafa, Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi kira na musamman ga' yan kasuwa da su sassauta kan farshin kayan abinci da ragowar kayan masarufi.
An yi taron ne a masarautar Zazzau, ranar Lahadi, in da Sarkin Kanon ya nuna irin alheran da 'yan kasuwa za su samu daga Allah idan su ka tausayawa bayinSa a wannan wata mai alfarma na Ramadhan.
Haka kuma ya kara yin kira ga mawadatan cikin al'umma da su taimakawa talakawa ganin yadda rayuwa ta kara zama a matse.
"Ina rokon' yan kasuwar mu kamar yadda na saba kan su dubi irin taimako da dauki da albarka da za su samu daga Mahaliccinmu idan su ka rage farashin kayan abinci da ragowar kayan masarufi. Musamman ganin kusantowar wata mai Alfarma na Azumin Ramadhan," in ji Sarkin.
Ya ce" Mu na rokon mawadatanmu da su taimakawa al'umma wajen rage musu radadi na wannan rayuwa. Cikin sahalewar Allah."
Sarkin ya yabawa Farfesa Gusau wajen fito da tarihin Daulolin Kano da Sakkwato da Zazzau da Zamfara da Katsina da Kebbi
An yi sowa sosai lokacin da Sarkin yake wannan kiran da yake nuna tausayi da son al'umma dake zuciyar Sarkin. Kamar yadda wasu jama'a da mu ka tattauna da su s**a fada jim kadan bayan tashi daga taron.
Mawallafin littafin Farfesa Gusau ya godewa Mai Martaba da duk iyayen kasa da su ka halarci taron.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Culinary Team
Attire
Telephone
Website
Address
Azare
071