Matattarai Labarai
29/05/2022
Jawabin Atiku Abubakar Na Farko Amatsayin Dan Takarar Shugaban Kasa Na PDP Azaben 2023
Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Yau ranace mai matukar tarihi kuma ranace da zata tabbatar da cewa Nijeriya ta kalli alkibula a zaben 2023, Cewar Atiku Abubakar
Bayan nasararsa a matsayin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya aika da sakon murna ga yan Nijeriya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce ya yi farin ciki sosai da kasancewar sa wanda zai daga tutar jam'iyyar adawa ta PDP a zabe mai zuwa.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben kasar mai zuwa, Alhaji Atiku Abubakar ya sha alwashin hada kan kasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya kuma dauki alkawarin magance matsalolin tsaro da na tattalin arziki da ke tunkarar kasar.
Atiku ya kuma yiwa gwamnatin APC wankin babban bargo cewa ta lalata duk wasu nasarori da gwamnatin PDP ta shimfida.
Adaran jiya ne jam'iyar adawa ta PDP ta sanar da nasarar Alhaji Atiku Abubakar na lashe zaben fidda gwani na shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyar ta PDP
Bayan sanar da nasarar Alhaji Atiku Abubakar a matsayin dan takarar shugaban kasa karkashin inuwar jam'iyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya sha al'washin maido da Nijeriya cikin haiyyacin ta idan har yan Nijeriya s**a zabe shi a matsayin shugaban kasa 2023.
Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne yayin da yake bayar da jawabin amincewarsa bayan an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwanin shugaban kasa na PDP.
Atiku ya caccaki jam’iyyar APC kan yadda ta mayar da nasarorin da jam’iyyar PDP ta samu a lokacin da ta ke rike da madafun iko baya, inda ya yi alkawarin gyara su idan aka sake zabar su.
Atiku Abubakar Ya ce: “Zan magance matsalolin tsaronmu a kasar nan. Na kuma dauki alkawarin tunkarar matsalolin tattalin arzikinmu. Jam’iyyar PDP ta sanya Nijeriya ta zama daya daga kasashe masu ci gaba da wadata a nahiyar Afirka.
Mun aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki da s**a kawo ayyukan yi, da wadata a kasar nan. Amma Jam’iyyar APC ta shigo ta goge duk wadannan nasarori. Shi ya sa na ce yau rana ce mai matukar tarihi a Nijeriya.
Domin hakan zai ba mu damar gyara duk wani rashin shugabanci na gwamnatin APC.
Ya kuma nemi hadin kan sauran yan takarar da s**a fadi a zaben fidda gwani, yana mai cewa babban abun da ke gaban mu yanzu shine kwato Nijeriya daga hannun jam’iyyar APC mai mulki.
Domin dukkan mu munyi imani cewa Nijeriya ta fada cikin wani hali a karkashin inuwar mulkin jam'iyar APC saboda haka ya k**ata musani cewa Nijeriya da yan Nijeriya na matukar bukatar hadin kan mu domin kawo karshin mulkin APC a yayin zaben 2023.
Atiku ya ce: "Bari na yi amfani da wannan damar wajen kira ga abokan takarata. Sannan na basu tabbacin cewa a shirye nake na hada kai da aiki tare da su sannan na basu damar taka rawa a wannan jam'iyyar da gwamnatinmu ta gaba.
Saboda haka ’yan uwana, ina son in yaba da kokarinku na zurfafa tsarin dimokuradiyya a tsarin wannan jam’iyya. Zaben fidda gwani ne mai inganci. Don haka, na yaba muku akan haka kuma ina fatan yin aiki tare da ku kai da kai. Ta yadda za mu gina wannan jam’iyyar tare zuwa matakin da za mu iya kwace mulki.
Atiku Abubakar ya kuma bayyana cewa fafutukar sake gina Nijeriya tare da inganta ta zuwa matakin ci gaba ya fara aiki daga yanzu da ya lashe tikitin takarar shugabancin kasar.
Acikin jawabin nasa Alhaji Atiku Abubakar ya ce yan Nijeriya zasuyi alfahari da shi a matsayin shugaban kasar Nijeriya idan har s**a zabe shi 2023.
01/04/2022
Babu labarin ganin jinjirin watan Ramadana ya zuwa yanzu, Cewar kwamitin ganin wata
Daga Abubakar A Adam Babankyauta
A daren yau Juma'a ne a kwamitin ganin wata na kasa ya bukaci musulmai a Najeriya su fara duban jinjirin watan Ramadana.
Ya zuwa yanzu, kwamitin ya ce bai samu labarin ganin wata ba daga wasu sassan jihohin kasar nan.
Kwamitin ya bayyana haka ne a cikin wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewar bayanin da ke neman jin ta bakin sauran al'umma, an ce:
Ya zuwa yanzu babu rahotannin da aka samu daga Bauchi, Gombe, Azare, Misau, Numan, Lagos, Kaduna, Abuja, Bajoga, Nafada, Maiduguri da dai sauransu.
Kwamitin ya kuma nemi jama'a da su ba da bayani sahihi daga yankunansu game da ganin jinjirin watan na Ramadana.
Jama'a ku tayamu yada wa domin sakon yakai zuwa ga al'ummar musulmai.
08/03/2022
Ƴan Ta'adda Sun Kashe Mutane 62 A Garin Zuru Dake Jihar Kebbi, Da Wasu Yankuna A Jihar Neja
..Ƙungiyar "Arewa Media Writers" tana kira ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa.
Daga Ƙungiyar "Arewa Media Writers"
Ƙungiyar marubutan Arewa "Arewa Media Writers" ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar na ƙasa Comr Abba Sani Pantami, tayi Allah wadai da kisan da ƴan ta'adda s**a yiwa al-ummar garin Zuru dake jihar Kebbi da wasu yankuna na jihar Neja da s**a haɗa da ƙaramar hukumar Rija'u da sauran su.
"Arewa Media Writers" tayi takaici da jimamin faruwar wannan mummunan ta'addacin da aka yiwa ƴan uwan mu dake yankunan.
Haka zalika ƙungiyar tana sake kira da kakkausan harshe ga gwamnatin Najeriya da ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar rashin tsaron da ya addabi yankin mu na Arewa, don al'ummar yankin su zauna cikin kwanciyar hankali.
Ƙungiyar "Arewa Media Writers" tayi Addu'ar samun rahama ga mamatan da s**a rasa rayukan su, wa ƴanda s**a rasa ƴan uwansu Allah ya basu ikon jure rashin.
Daga ƙarshe Ƙungiyar tana Addu'a tare da rokon Ubangiji ya kawo mana zaman lafiya mai ɗorewa a yankin mu na Arewa dama ƙasar Najeriya baki ɗaya. Amin
05/03/2022
Hattara Al'ummar Musulmai
Daga Abubakar A Adam Babankyauta
Muna masu kira ga al'ummar musulman Nijeriya da ma na duniya baki daya da su kula da irin kalan kayan da za su siya su sa a jikin su. Domin akwai sabbin kayan sawa t-shirt t-shirt da s**a shigo cikin Nijeriya musamman kudancin Nijeriya masu dauke da sunan Allah a jikin su.
Wannan daya daga cikin irin t-shirt din da muka gano kenan wanda wani bawan Allah Musulmi ya siyo domin ya yi ado da ita anan cikin Abuja.
Lallai ya k**ata al'ummar Musulmai su sa ido akan irin kayan da zasu siyo susa a jikin su domin gudun kada susa kaya masu sunan Allah da Manzon Allah S.A.W a jikin su.
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Website
Address
Asokoro
08030471966