Labarai soyayya com

Labarai soyayya com

Share

27/12/2025

Gawani kyeuta dukkan wanda ya ammasamin dedei Yana da kyeuta menene wannan Kaine Mai abun Amma mutane sunfika aiki dashi

25/12/2025

Barka da kasancewa cikin wannan rana masoyiyata. Dukanin rayuwata na karanta, nayi Mafarkinta, na jirata, nayi kuka don ita,

yanzu haka na gano kece kadai abar kaunata. Tun farkon haduwata dake zuciya ta aminta dake a matsayin mai debe mata kewa. Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.

Nasan burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana. Ina son ki fiye da zinariya.

Wa kafi ƙauna? na ce, wannan da ta ɗauke ni wata tara a cikinta, ta haife ni tana farin ciki, sa'annan ta kyautata tarbiyata....

Episode 7$/&8Wannan ita ce soyayya ta har abada, ba ta tsufa b***e ta mutu!

25/12/2025

Episode 5&6Kyakykyawar zuciyar kice ta bayyana kyawawan halayyar ki, wadanda suke sakamin cikakkiyar nutsuwa a cikin ruhina Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.

Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. kasantuwar mu a raye cikin ruhi guda d’aya ya sanya zuciyoyin mu bugawa cikin lokuta makamanta juna.

Komai na mu ya kasance yana faruwa ne a lokaci guda hatta ba’kin ciki da kuma farin-ciki, wato ruhi d`aya gangar jiki kuma biyu. Farin cikin ki shi ne nawa, ina son ki.

Tabbas Ubangijina ya cancanci yabo ta kowacce fuska, bayan ni'imar rayuwa da ta lafiya da yayi mana, sai kuma ya kara mana da baiwar kasantuwar sanyin idanun mu a cikinmu, wadda muke kalla muji nutsuwa ta sauka a jikinmu, muji tabbas muma wasu mutane ne masu daraja, saboda kasantuwar me daraja a cikin mu.

Kai don Allah kuce ALLAHU AKBAR!!!🥰🙈💋💞

25/12/2025

Episode 3&4Kowa ne dare nakan koma gida ina kuka saboda nasan bazan kara ganin kiba har sai gobe Shin rana ce ta fito ko murmushin kine?

Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya,

ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.

KUZO MU YABI UBANGIJI! Ya zama wajibi mu bude safiyarmu da fara salati ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam, muyi Tasbihi da Hamdala a wajen gwani wajen iya tsara halitta, gwanin da idan ka kalli halittarsa sai ka rasa ta wanne wuri zaka fara yabo a gareshi, saboda yakai makura wajen kagar halittar da kyawunta ke d'aukar hankalin duk wani me lafiyayyen tunani da idanun gani!

Tabbas Gwanina Allahu, shine Allahu, shine me halittar akwai daga babu, ya samar da kyawu a inda babu shi, ya samar da nagarta a wurin da babu ita, ya samar da daukaka a cikin makaskanta, ya saukar da baiwarsa ta kamala da cikar haiba tare da zunzurutun Kyau akan wanda ya zaba a cikin halitta,

25/12/2025

Episode 1Duk sarakunan mata dake mulkin zuciyoyin masoya babu wata zuciya da ta kai tawa samun sarauniya mai adalci kamar ki. kece ruhina, kin zamto farin cikin raina

A kullum bani da burin sauraren wani zance in ba naka ba Zamo na kowa koda kowa bai zamo naka ba. Yiwa kowa fatan alheri koda akwai masu yima fatan sharri, saka dukkanin musulmi acikin addu arka koda babu mai sakaka acikin addu`arsa.

Nufi kowa da alheri koda akwai masu nufarka da sharri. kyautata tsakaninka da Allah kada kadamu da abinda mutane suke cewa akanka. Allah ya kyautata rayuwarmu Amin

Asali zuciyar mace kyakkyawa ce, nagartacciya, wadda babu komai a cikin ta sai haske tare da kyautatawa ga dukkan wanda ya shigo rayuwar ta, bata san cin amana ko ha'inci gami da yaudara ba,

Idan har kaga zuciyar mace ta rikide daga asalinta na kyawu da nagarta zuwa gurbatacciyar da take ha'intar dukkan wanda ya shigo rayuwar ta, to ka duba farkon lamarin, zaka samu namiji ne ya jagoranceta zuwa ga gurbacewa, amman zuciyar mace bata tab'a gurbacewa ba tare da sanya hannun namiji ba.

25/12/2025

Episode 1 SO YA FI YIWA MATA ILLA.



1. Duk da cewa, Mace tana da yawan Hakuri da Juriya, amma hakurin ta ya ta'allaka ne kurum kan abinda take matukar So. Tana da Hakuri da kuma jure dukkan kalubalen Rayuwa, amma ba ta da Hakurin Jure yaudara ko kaddarar da za ta raba ta da wanda ta zurfafa matuka cikin kaunar sa. Hakurin ta, ba ya hanata illatuwa daga soyayya.



2. Mace tana da Zuciyar da zan iya kira da "Kuran Soyayya", ba ta bukatar lokaci mai tsawo kafin ta faɗa cikin Soyayya. Cikin lokaci kankani za ta faɗa, kuma har ta zurfafa a ciki. Sai dai tana sintar kan ta cikin mawuyacin hali kafin ta iya fita daga tafkin So.



3.*ina da shawarwari ga duk Macen da soyayya ta illata mata Zuciya.



A. Duk da cewa Allah (SWT) shi ke da ikon sarrafa dukkan komai, amma ya ba mu ikon sanyawa da kuma fitar da komai a cikin Zuciyar mu. Idan kina son ki sanya wani a cikin Zuciyar ki, ki tabbatar kin mallaki rabin abinda ya mallaka, - na Ilimi, Arziki, Nasaba, da kuma Nagarta. Kuma ki tabbatar kin ninka shi a kyau!. Yin hakan zai hanaki sanyawa Zuciyar ki Ruwan guba. ❤



B. Mu Maza muna son Macen da take da Halaye (Ma su kyau!) kwatankwacin na Mahaifiyar mu. Wannan dalilin ne yasa, wasu Mazan su ka damka wa Mahaifiyar su Mabuɗan Zuciyar su. Saboda haka, idan kika siffantu da ɗabi'ar Mahaifiyar wanda k**e so, kamar kin samu mabuɗin Zuciyar sa ne.



C. Kar ki zurfafa matuka a cikin Son wani Namiji, in ma kin zurfafa, kar ki bayyana. Domin mu Maza ba mu cika girmama tare da daraja waɗanda s**a nuna sun zurfafa a cikin soyayyar mu ba. Mun fi daraja wacce za ta gasa mana aya a Hanu.



D. Kar ki dukar da kan ki cikin kunci da kunar Zuciya, saboda wani Namiji ya yaudare ki. Ki ɗaga kan ki cikin karfin guiwa da fatan Allah (SWT) ya warkar da Zuciyar ki. Sannan ki yi dubi zuwa ga Mazan da suke shirye su faranta miki ta hanyar sanya ki cikin Lambun Soyayya. ❤



E. Ki buɗe Zuciyar ki, ki amshi Soyayya. Duk halittar da k**e gani a wannan Duniyar, So ya kuntata mata, ko kuma

Want your university to be the top-listed University in Ajegunle?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Address

Kurmiishaq54@gmail. Com
Ajegunle
[email protected]