Duniya INA Labari
10/07/2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ƙaimi wajen tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan Nijeriya rajistar shaidar ɗan ƙasa ta dijital a faɗin ƙasar, ta hanyar ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa (NIMC).
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba a Abuja yayin da ya karɓi baƙuncin Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, da tawagar ta, waɗanda s**a kai masa ziyarar girmamawa domin gabatar da muhimman tanade-tanaden sabuwar Dokar NIMC ta 2026.
Ministan ya ce ingantaccen tsarin tantance shaidar 'yan ƙasa yana da matuƙar muhimmanci wajen kyautata shugabanci, tsara cigaban ƙasa, bunƙasa harkokin kuɗi, haɓaka sauyin fasahar zamani da kuma aiwatar da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce: “Tsarin tantance shaidar 'yan ƙasa shi ne ginshiƙin ajandar sauye-sauyen Shugaban Ƙasa. Domin idan za a aiwatar da gyare-gyare, dole ne a san waɗanda ake yi wa. Idan ba a san adadin jama'a ba, da tsarin yawan su da yadda s**a kasu, ta yaya za a tsara musu ingantattun tsare-tsare?”
Idris ya yaba wa shugabancin Dakta Coker-Odusote, yana mai cewa yi wa sama da mutum miliyan 136 rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan mutum miliyan 100 da ba a yi wa rajista ba.
Ya ce: “Mutum miliyan 136 da aka riga aka yi wa rajista babban cigaba ne, amma har yanzu akwai kusan 'yan Nijeriya miliyan 100 da s**a rage, kuma su ma ya kamata a yi musu rajista. Kowane ɗan Nijeriya ya cancanci a saka shi cikin tsare-tsaren cigaban ƙasa.”
Ministan ya ce cimma burin yi wa kowa rajista yana buƙatar ci gaba da wayar da kan jama'a, musamman a matakin ƙananan hukumomi da al'ummomi. Don haka ya buƙaci NIMC da ta ƙara haɗin gwiwa da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), wadda ke da ofisoshi a dukkan ƙananan hukumomi 774 na ƙasar nan.
Ya ce: “Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa ita ce mafi dacewa wajen isa ga al'ummomin karkara. Ina roƙon ku da ku ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar ku da NOA domin mu duka mu tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya ya fahimci muhimmancin tsarin shaidar 'yan ƙasa.”
Haka kuma ya yaba wa NIMC bisa yadda ta kiyaye bayanan jama'a, yana mai cewa babu wani rahoton kutsen da ya yi sanadin fallasa bayanan masu rajista.
Ya ƙara da cewa: “Na yi farin cikin jin cewa ba ku taɓa fuskantar matsalar kutsen bayanai ko da sau ɗaya ba. Kare sirrin bayanai, gudanar da aiki cikin gaskiya da kuma amincewar jama'a su ne ginshiƙan nasarar tsarin shaidar dijital, kuma za mu ci gaba da amfani da dukkan kafafen yaɗa labarai na Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai wajen tallafa wa shirye-shiryen wayar da kan jama'a.”
Tun da farko, Darakta Janar na Hukumar Wayar da Kan Jama'a ta Ƙasa (NOA), Mallam Lanre Issa-Onilu, ya tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da tallafa wa NIMC wajen wayar da kan jama'a ta hanyar cibiyoyin ta da ke faɗin ƙasar nan.
Ya ce: “Mun san muna aiki tare, amma ina fatan za ku ci gaba da tuntuɓar mu domin mu ga yadda za mu ƙara ba da gudunmawa. Muna da wakilci a wuraren da kuke son zuwa domin wayar da kan jama'a da faɗakar da su.”
A nata jawabin, Babbar Darakta ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote, ta ce sabuwar Dokar NIMC ta 2026 ta sabunta tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya, inda ta ƙunshi tanade-tanade kan kare bayanai, tsaron intanet, inganta tsarin bayanan gwamnati na zamani da kuma ƙarfafa amincewar jama'a da tsarin dijital.
Ta ce: “Shugaban Ƙasa ya umurce mu da mu fara rajistar jama'a daga unguwa zuwa unguwa, domin yana son tabbatar da cewa mutanen karkara da na matakin al'umma ba a hana su cin gajiyar duk wani shirin tallafin gwamnati ba.”
Ta bayyana cewa hukumar ta fara gangamin rajista a dukkan unguwanni 8,809 na Nijeriya domin tabbatar da cewa an yi wa kowane ɗan ƙasa rajista, ciki har da mata, yara, masu naƙasa, mazauna karkara, 'yan gudun hijira, baƙin da ke zaune bisa doka da kuma 'yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje.
A nasa jawabin, Shugaban Sashen Hulɗa da Jama'a na NIMC, Dakta Kayode Adegoke, ya ce sabuwar dokar ta sauya tsarin kula da shaidar ɗan ƙasa a Nijeriya baki ɗaya.
Ya ce: “NIMC ta wuce matsayin mai adana bayanai kawai, ta zama babbar hukuma ta ƙasa da ke da alhakin kula da tsarin shaidar dijital. A yanzu, NIMC ita ce kaɗai hukumar da aka ba ikon kula da tsarin shaidar dijital a Nijeriya.”
Ya ƙara da cewa dokar ta samar da tsarin doka na Digital Public Infrastructure (DPI) da Public Key Infrastructure (PKI), tare da ƙarfafa kariyar bayanan jama'a da faɗaɗa amfani da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) a ayyukan gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su.
A cewar sa, NIMC ta haɗa tsarin ayyukan ta da fiye da ma'aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati 250, tare da ƙaddamar da sababbin fasahohi da s**a inganta ayyukan rajista tare da rage lokacin da ake ɗauka wajen yi wa jama'a rajista.
Ziyarar ta samu halartar Darakta Janar na NOA, Mallam Lanre Issa-Onilu; Babbar Darakta kuma Babbar Jami'ar Gudanarwa ta NIMC, Dakta Abisoye Coker-Odusote; Daraktan Sashen Samarwa, Wallafe-wallafe da Adana Takardu, Mista Ibidapo Okunnu; Mataimakiyar Darakta mai kula da Hulɗa da Jama'a da Ladabi, Misis Fatoke Folasade, da sauran manyan jami'an Ma'aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da na Hukumar NIMC.
Ma'aikaci NECO Wanda bandits s**a sace kan hanyar gumi zuwa kajiji jiya ,sanadiyar barin wutar da akayi bandits ,jami'an tsaro sun kubutar dashi.
Umar Gidado Gummi
Click here to claim your Sponsored Listing.
Category
Contact the business
Telephone
Address
Abuja
SOKOTO,KANO,KADUNA,ABUJA,KATSINA,LAGOS