Yantacciya

Yantacciya

Share

17/06/2025

Kaso 70 na ƙarfin Amrk na sama da ruwa ya tunkari Yammacin Asiya inda za a yi Jana'izar Tinƙahon Duniya.

Za su iya yin amfani da MOAB (Mother of all Bombs) a kan Ira*n.

Deep state ta anshe ragamar jagorancin Amrk. Mahaukacin Kare ya rusunawa masu gidansa, sun shafi kansa sun ce good boy.

To daga nan ne Jahimu za ta buɗe, ba akan Iran kaɗai ba, a kan Duniya.

Kusan shekara guda guda kenan munata rubutu a kan abun nan. Har Alƙalami ya fara gajiya.

Ba tsorata Mutane muke son yi ba.
Amma kowa ya sani, ba taɓa sauya Order ta Duniya ba tare da an yi uwar watsi ba.

Gumurzu ne zai fara tsakanin great reset da great awakening. Tsakanin globalist north, da global south. Yanzu muna a baƙin gate a tsugunne, muna jiran a buɗe kofa. Idan an buɗe ba za ta rufe ba sai kowa ya shiga.

الملحمة

Yawan ƙarafa na faɗa an fi Iran. Ba yawan ƙarfi ba. Ƙarfi na Allah ne kuma ya bawa muminai.
Tabbas Iran za ta jigata. Amma za ta buwaya.
Al'amari ne zananne, tun ranar gini.

Shamsudeen Hassan

09/04/2024

DAN AREWA DA WAWAN TUNANI 2

Zanga Zanga wani aikine da ya kunshi bayyana mastayar wani mutum ko gungun mutane akan wani abu a bayyane ta hanayar Furtawa ko nunawa domin jama'a su shaida.

Irin wannan ta faru a ranar da aka bayyana Addinin Musulunci a sarai, inda Sahabbai s**ayi Jerin Gwano Daga gidan Arqam bin Abul Arqam (R.A)
inda musulmai suke Yin taron Addini a asirce, zuwa jika dakin Ka'aba mai Girma .
suna Shelanta wadannan Kalmomi

"Allah Ɗayane Kuma Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wa Alihi Manzonsa ne"

Ana jifansu ana Dukansu , haka s**aci gaba da wannan Jerin Gwano Har Jikin Dakin Ka'aba mai Daraja.

Halasci Ko Haramcin Zanga Zanga a Musulunci ya dogara ne da sakon da Zanga Zangar take isarwa.
Sakon Halas ne ko Haram, shine zai Fassara Zanga Zangar a Shari'ance.

Domin A addinin Musulunci komai Asalinsa Halas ne , har sai an sami Haramcin aikatawa.

Shin Zang-Zanga tana da Amfani kuwa wajen kwatar kai daga Kangin Bauta ?

Eh tabbas Zanga Zanga tana da Amfani kwarai da gaske, domin itace kadai hanaya ta kwanciyar hankali wacce Al'umma suke iya bayyana matsayarsu akan wani abu ba tare da sun cutar da kowa ba.

Wannan Tsarin na Bayyana matsayar Al'umma itace ta Bambance Bawa da 'Yantacce, itace ta banabance wayayye da Kidahumi, itace ta Bambance Wanda yasan ciwon kansa da wanda bai sani ba.

Zanga Zanga ta samar da Mafita ga Al'ummomi masu yawa, akan wasu tsare-tsaren da aka dankara masu wanda yake tauye masu hakki.

Misali shine Zanga Zangar da kungiyoyin gwagwarmayar Africa ta Kudu s**ayi ta Allah wadai da nuna wariyar launin fata a Afrika ta kudu.
Wanda aka fara tun 1912 har 1992 Ya zama jigo ga gwagwarmayar neman 'Yancin Africa ta Kudu, kuma sila A samun 'Yancin kansu.

Zanga Zangar da Akayi a Nigeria ma Lokacin mulkin Jonathan akan kara kudin man fetur tayi tasiri, domin kuwa tasa dole ya janye kudirin karin kuɗin man a wancan lokacin.

Shin Zanga Zanga a Nigeria akan wani abu da yake faruwa a Duniya Tana da wani Tasiri a wancan muhallin ?

Eh tabbas duk daga inda kayi Zanga Zaga a Duniya domin nuna goyon baya ga wasu al'ummar da ake zalunta to yana taimakawa waɗan da aka zalunta ta ta hanyoyi masu yawa, daga ciki akwai karfafa Gwiwa cewa Ba'a manta dasu b akwai waɗan da s**a tare dasu a neman 'Yancin da suke , basu kaɗai bane.

Waɗan da suke zaluncin suna na muradunsu a kowacce kasa a duniya, dan haka duk ƙasar da al'ummar ta duk fito s**ayi Allah wadai da Zaluncin da akewa raunana a wani waje to Ita kasar da take aikata wancan Zaluncin tana da wakili a kasar da kake Kuma sakon ka yaje gareshi , kuma sun tabbatar baka tare dasu a Zaluncin da suke, kuma zaka taimakawa waɗan da ake zalunta Daduk abinda kake iyawa, Hakan Barazana ce Babba Ga Azzalumi.
Domin Munga yadda Zanga Zangar da akayi a Libiya Yankin Bengazi ta shafi Amurka kai tsaye, har ta ki ga rufe Ofishin Jakadanci na Amurka a Libya ɗin.
Kuma mmunga yadda zanga Zanga tasa Amurka da Isara'ila sake Mugayen manufofin su masu yawa a Iraq, Jordan da sauran ƙasashen da s**a yadda da yin wani yunkuri domin kawo sauyi.

Shin Idan Aka samu Nasarar Kwace wa Al'umma'Yancin yin Zanga Zanga mai zai iya biyu baya ?

Idan Al'umma Ta yadda aka kwace mata 'Yancin yin Zanga Zanga to an maida wannan Al'ummar K**ar bayi, domin za'ayi ta korasu kamar dabbobi babu Mai kiwo, kuma basu da wata hanya ta nuna rashin amincewarsu akan wani tsarin da aka dankara masu.
Shiyasa Azzaluman masu mulki s**a dukufa wajen ganin sun Raba Al'umma da wannan 'Yancin da Addini ya basu kuma Tsarin Mulkin Demokradiyya ya basu.
domin ta Hakane kadai cikakkiyar bautarwa zai yiwu akan wannan Al'umma.

Rushin Gwagwarmaya da kwatar 'Yanci daga Azzaluman masu mulki shine kadai zai bawa duk wani mai son ya rayu cikin 'Yancin Addini da zamantakewa, Mafita da yake nema domin rayuwa cikin Aminci.

~Ibn Abubakar Alhausawy

27/02/2024

KAFIN MU SAMI 'YANCI SAI MUN NEMI 'YANCI (2)

A Rubutunmu na Farko Munyi bayanin yadda masu Bautar da Al'umma suke karantar ta ciki da bai, kafin su bautar da ita, ta yadda Bazasu sami Turjiya ba daga waɗan da suke Bautarwar, inda wasu da ake bautarwar ma su kansu Basusan ana bautar dasu ba.

Matakin Da Masu mulkin mallaka suke bi domin tabbatuwar mulkinsu.

To bayan Masu mulkin mallaka sun karanci Al'ummar da suke yiwa mulkin mallaka to akwai hanyoyin da suke bi domin Tabbatar da wannan mulkin nasu, daga karantar Al'ummar da Sukayi, tunda sunsan Karfin Al'ummar da kuma Raunin ta.

Hanyoyin da 'Yan Mulkin Mallaka suke bi wajen Sarrafa Al'ummar Nigeria, Africa dama duk inda suke mulkin mallaka a duniya.

Tsarin Mulki: Soja Ko Farar Hulla ko Sarauta.
Wajen Tsarin Mulki suna samar da tsarin mulki ne da bazai taɓa cin karo da Muradunsu na mulkin mallaka ba, koda kuwa su waɗan da ake mulka suna tsammanin suna da 'yanci , to duk abinda zasuyi bazai wuce iyakar da 'Yan Mulkin Mallaka s**a shata musu ba, inde kuwa basu tsallaka wannan iyaka ba, to tsarin mulkin bazai amfani al'ummar ba.

Zabar Shugaba:
Wajen Zabar Shugaba da zai jagoranci wannan tsarin da 'Yan Mulkin Mallaka s**a yiwa sitamfi wanda bazai amfani Al'ummar kasar ba, suna tabbatarwa Shugaban Zaiyi biyayya ne ga Tsarin da aka bashi (Na mulkin mallaka) Kuma bazai ketare iyakar da aka shimfida ba.
domin tabbatar da biyayyar Dan takarar wannan kujera ta mulki to dole yaje can kasashen 'Yan Mulkin Mallaka domin amsa tambayoyin da Zasuyi masa, wanda daga nan zasu gane Zaiyi biyayya ko A'a.
Shiyasa Lokacin Zabe ko nadin sarauta zakuga ana rige rigen zuwa kasashen waje tarukan tattaunawa, To
idan Mai Neman Mulkin Zaiyi biyayya to sai a bashi damar takara, idan yaci mulki su saka shi cikin rabon arzikin da zasu deba daga kasarsa, Sannan su bashi kariya shi da iyalansa daga tuhumar cin hanci da rashawa, Sai yayi Komai ba komai, Anan duniya, idan bazai yi biyayya ba kuma to wajen zaben fidda gwanima dakyar ya wuce inka ya wuce to bazai wuce Babban Zabe ba, Inko duka 'Yan takarar sun yarda da sharadinsu to sai su zabi wanda Zaifi yin biyayya su bashi mulki.
inko bayan yahau kan mulki ya nemi bijirewa, to sun shirya yadda zasu kau da wanna mai mulkin, ta hanayar amfani da turakun tsarin mulkinsu da yake jagoranta.
Irin wadannan turakun Mulkin sun hada da Soja, Majalisa, da sauransu.

Tsaron Kasa:
Kasashe'Yan Mulkin Mallaka basa taba bari tsaron kasashen da suke mulka yabar hannunsu.
sune suke Bada training ga Askarawa na kasa, suke sayar mata da makamai, suke kula da cibiyoyin tsaron kasar da sunan masu bada shawara, suke Bada umarni wajen ayyukan tsaro na wanan kasa, dan haka duk yadda za'ayi Kasar tsaronta yana tafin hannunsu.
Idan sunso sai su samar da rashin tsaro domin biyan wasu bukatunsu kuma babu wanda ya isa ya samar da tsaron.
Duk sirrin Kasa yana hannunsu. dan haka dolen masu rike da mulkin kasar suyi musu biyayya sau da kafa.
Abin takaicin ma Duk training din da zasu bawa sojan wannan kasa to marar amfani zasu bashi, haka duk makamin da zasu bashi to shima marar amfani zasu bashi domin karma yayi tunanin kalubalantar su wata rana.

Tattalin Arziki:
Kasashe 'Yan mukin mallaka, Sune suke Tasarrufi da tattalin arziki na ƙasashen da suke mulka, sune suke da Bankin Bada Lamuni na Duniya Wato (IMF) sune suke da Bankin Duniya da yake tsarawa dukkan sauran Bankunan ƙasashe yadda Zasuyi aikinsu wato (World Bank), sune suke da cibiyar hada-hadar kudade ta duniya wato (World Trade Center) sune suke da Hanyar musayar kudi a tsakanin Bankunan duniya wato (SWIFT) sune suke da Kudin da dole idan zakayi cinikayya ta kasuwanci sai dashi wato(Dollar) Koda kasuwanci Kasa zatayi to Saide ta siyar ko ta sayo kaya ta amfani da kuɗin kasashe'Yan Mulkin Mallaka.
dade sauransu.
Shiyasa sai talaka ya rasa Meye Dalilin da yasa kudin kasarsa kullum yake rage daraja.
duk wadannan cibiyoyin kayan aikine na tabbatar da Mulkin Mallaka ga kasashen da ake yiwa mulkin mallaka.
Dolen kasa tayi biyayya ga dokoki da Muradun 'Yan Mulkin Mallaka, inkuma taki su saka mata takunkumi (su hanata cinikayya a duniya)

Sanna Har yau dinnan Kasashen da Ba'ayi masu mulkin mallaka to basu da yawa ko Goma dakyar su kai.

Nan Munyi takaitaccen Bayani ne akan abubuwa da s**a shafi kasa kai tsaye , wanda su masu mulki sun san dasu, kuma sunayin biyayya ga Iyayen Gidansu 'yan Mulkin Mallaka, to amma Meyasa Koda talakawa sun gane anayin mukin kasar sune ba domin su talakawa su sami saukin Rayuwa ba, kuma basu da wata dama tacewa ayi ko a'a a al'amuran Tafiyar da kasarsu , Amma duk da hakan talakawa basa iyayin komai ?
Ko Meyasa kaso mafi yawa na al'ummu sunsan mulkin mallaka ake musu amma basa iya yunkurin kawo Gyara ?

Insha Allahu zamu amsa wadannan tambayoyi a cikin Rubutun mu na gaba , da Zaiyi magana akan yadda 'Yan Mulkin Mallaka suke sarrafa Al'ummar Gari Domin su hanasu kokarin kawo sauyi.

~Ibn Abubakar Alhausawy

Want your business to be the top-listed Media Company in Abuja?
Click here to claim your Sponsored Listing.

Telephone

Website

Address

Amfanuwa Duniya/lahira
Abuja