Al'umar Arewa
Wani matashi wanda Gwajin Genotype yake nema ya Raba shi da Budurwarsa da s**a kwashe Shekaru suna Buga Soyayya.
24/06/2026
24/06/2026
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Kudirin Kafa ‘Yan Sandan Jihohi
Majalisar Dattawa ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa ‘yan sandan jihohi a fadin kasar nan.
24/06/2026
DSS ta ba da umarnin binciken jami’an da s**a ja Sowore a Kotu
Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta ba da umarnin gudanar da bincike kan jami’anta da aka gani suna jan ɗan gwagwarmaya kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar AAC, Omoyele Sowore, bayan zaman kotu a Abuja.
Kotun tarayya da ke Abuja ta umarci a tsare Sowore a gidan gyaran hali na Kuje har sai an saurari ƙarar da ya shigar kan soke belinsa. Alƙali Mohammed Umar ya yanke hukuncin ne bayan ya yi watsi da bukatar Sowore ta janye kansa daga shari’ar bisa zargin nuna son kai.
Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna wasu jami’an DSS masu ɗauke da mak**ai suna jan Sowore daga harabar kotu, lamarin da ya jawo s**a daga jama’a.
A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun DSS, Favour Dozie, ya ce shugaban hukumar ya ba da umarnin gaggauta bincike kan halayen jami’an da abin ya shafa. Ya kuma ce Sowore ne da kansa ya zaɓi shiga motar DSS maimakon ta hukumar gidajen gyaran hali bayan faruwar lamarin.
DSS ta ce tana tuhumar Sowore ne saboda wasu kalamai da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta inda ake zarginsa da kiran Shugaba Bola Tinubu “mai laifi”. Hukumar ta ce tun a shekarar 2025 ta nemi ya janye kalaman nasa kafin daga baya ta kai ƙarar kotu domin neman fassarar doka kan hakkin yin irin waɗannan kalamai kan shugaban ƙasa.
Daily Nigerian Hausa
Click here to claim your Sponsored Listing.