REAL Dan Mashi
23/09/2023
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya, ya ce kasashen Afirka ba za su amince da yadda manyan kasashe ke fakewa da sunan kare ‘yancin dan Adam, suna hana su hukunta masu kwashe musu albarkatun kasa ta barauniyar hanya ba.
Tinubu da ke jawabi a taron Majalisar Dinkin Duniya, ya ce hakan na hana Afirka samun ci gaban tattalin arziki.
23/08/2023
Me Ya Sa Nijeriya Ke Neman Shiga Tsarin BRICS?
Daga Abdulrazaq Yahuza
Yanzu haka ana gudanar da taron kolin kasashen kungiyar BRICS (Brazil, Russia, India, China and South Africa) karo na 15 wanda Afirka ta Kudu ke karbar bakuncinsa. A shekarar 2009 ce aka kafa hadin gwiwar BRIC (Brazil, Russia, India da China), daga bisani bayan shigar Afirka ta Kudu a watan Oktoban shekarar 2010 aka mayar da sunan ya zama BRICS.
’Yan Nijeriya da dama masu kishin ci gaban kasar, sun yi na’am da yadda kasar ta nuna sha’awar shiga hadin gwiwar BRICS tare da takwarorinta na sassan duniya su 40, kamar yadda Jakadan Afirka ta Kudu a hadin gwiwan na BRICS, Anil Sooklal ya ayyana wa manema labarai kwanan baya.
Tambayar da wasu ke yi ita ce, me ya sa Nijeriya ke neman shiga wannan hadin gwiwa na BRICS? Galibin amsar da masharhanta ke bayarwa ita ce, kasar tana neman mafita a kan yadda za ta samu sukunin bunkasa tattalin arzikinta da kuma saukaka yawan dogaron da ta yi da dalar Amurka.
Nijeriya na so ta ci gajiyar hadin gwiwar BRICS kamar takwararta ta Afirka ta Kudu da ta samu ci gaban kasuwanci da kawayenta da kashi 10 cikin 100 a tsakanin 2017 zuwa 2021. Sannan hada-hadar kasuwancinta da kasashen BRICS sun bunkasa daga kudin kasar Rand Biliyan 487 a shekarar 2017 zuwa Rand Biliyan 830 a shekarar 2022.
Haka nan shigarta hadin gwiwar, zai bude mata sabon babin ci gaba ta bangaren bincike da kirkire-kirkire, makamashi, kiwon lafiya da bangaren ilimi. Tuni, har Afirka ta Kudu ta ci gajiyar ayyukan bincike sama da 100 a karkashin BRICS.
Bayan haka, kasancewar an kiyasta kayan da kasashen na BRICS ke fitarwa za su kai kashi daya bisa uku na duniya nan da 2030, sannan su ne ke da kusan kashi 18 cikin 100 na cinikin duniya, da mallakar kashi 26 cikin 100 na fadin duniya da kuma kusan kashi 42 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, Nijeriya za ta samu karin masu zuba jari daga kasashen hadin gwiwar baya ga bunkasa fitar da kaya zuwa waje.
Har ila yau, bisa irin rawar da Nijeriya ta taka a Afirka tun fil’azal, kamar shiga gaba wajen taya Afirka ta Kudu yaki da wariyar launin fata, da kashe wutar yakin basasa a Liberiya da Saliyo da gudunmawarta ga ayyukan kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya, shiga hadin gwiwar na BRICS zai kara ba ta damar samun fada a ji a duniya musamman kan shirye-shirye da tsare-tsare na kashin dankali da Turawan yamma ke amfani da su.
Tabbas, BRICS hadin gwiwa ne na kasashe masu muradin ’yantar da kansu daga tsarin rashin adalci na kasa da kasa, ita ma Nijeriya na so a dama da ita!
22/08/2023
ALBISHIR GAMASU LIZIMTAR KARATUN ALQUR ANI
1. Kyakkyawan Hadisi Daga Manzon Allah (Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ce: 'Idan mutum ya mutu danginsa s**a shagaltu da jana'izar sa,wani kyakkyawan mutum zai tsaya a kansa a Lokacin da ake rufe jikin mamaci, wannan mutumin yakan shiga tsakanin mayafin da kirjin mamacin.
Lokacin da aka gama binne sa, mutane s**a dawo gida, mala'iku 2, Munkar da Nakeer (Mala'iku biyu na musamman masu tambayar kabari), zasu zo cikin kabarin sa suna kokarin raba wannan kyakkyawan mutumin da mutumin da ya mutu, don su sami damar yi wa mamacin tambayoyi a game da imaninsa.
Ammaa kyakkyawan mutumin nan zai ce, 'Abokina ne shi. Ba zan barshi shi kaɗai ba. Idan an nada ku don yin tambayoyi, kuyi aikinku. Ba zan iya barin shi ba sai na shigar da shi Aljannah '.
Bayan haka sai ya juya ga abokinsa (mamacin nan) ya ce, 'Ni ne Alkur'ani, wanda ka saba karantawa, wani lokacin da babbar murya wani lokaci kuma da karamar murya. Karka damu. Bayan Munkar da Naker sun game maka tambayoyi, ba za ka sami baƙin ciki ba. '
Lokacin da Munkar da Nakir s**a ƙare tambayoyin su ga wannan mamacin, sai kyakkyawan mutumin nan ya shirya masa daga Al-Mala'ul A'laa, shimfiɗar siliki cike da miski.
2. Annabi (SAW) ya ce: 'A ranar sakamako, a gaban Allah babu wani Mai Ceto da zai sami matsayi sama da Alkur'ani, ba Annabi ko Mala'ika.'
3. Don Allah a tura wannan 'Hadisin' zuwa ga Yan uwa muslmai .... saboda Annabi (SAW) ya ce: 'Ka bada ilimi daga wurina ko da aya ɗaya ce'. Allah Ya bamu iko.Ameen
4. Muna addu'ar wannan sakon da muka kawo zai isa zuwa ga musulmai akalla miliyan biyar a duk faɗin duniya cikin kwanaki bakwai (7) masu zuwa, Insha-Allah. Da fatan za a tura wannan sakon a YAU ga abokai da dangi dan samun lada mai yawa daga Allah (SWT).
* Idan ka dauki Al-Qur'ani, Shaidan yakan kamu da ciwon kai.
* Idan Ka buɗe shi, sai ya fadi.
* Idan Ka karanta shi, sai ya suma.
* In kukayi kokarin tura wannan sako na Alkairi, zaiyi kokarin sanyaya muku gwiwa.
Cliquez ici pour réclamer votre Listage Commercial.
Type
Contacter l'entreprise
Téléphone
Site Web
Adresse
Matadi